Paru le 09/04/2021 | Broché 76 pages
Public motivé
Wannan bayani ya kumshi abubuwan da suka shahi yarintar Fatimane Moussa-Aghali musamma : tunani, wasanni da kuma zuwanta na farko makarantar boko.
Tun daga farko, wannan littafi, aiki ne da ta rubuta lokacin da ta ke karatu a Makarantar Harsunan kasashen Gabas mai suna INALCO, a birnin Paris, ta rubuta shi tare da farfesa Malam Claude Gouffé (Allah jikan ransa). A karshe, ta wallafa wannan aiki cikin mujallar Binndi e jande a shekara 1982 da shekara 1983. Kuma a shekara 2000, kungiya mai suna Albasa, a Yame, ta buga shi, ta yi shi littafi guda.
A kasar Nijar, con Bonkuku aka aifi Fatimane Moussa Aghali. Yanzu dai ta na Faranshi da zama. A INALCO ta koyi rubutun Buzanci, Fiausa da Hillanci, kuma ta yi doctorat a Sorbonne Paris III. Yanzu ta na aiki a kan Hausa, kuma ta na rubuta tatsiniyoyi sabiìin yaran makarantun boko da kuma karfafa harsunan gargajiya.